Harkar ilmi: Tsohon Shugaban kasa Abdussalami Abubakar ya yabawa El-Rufai
- Gwamna Nasir El-Rufai ya samu kwarin gwiwa na kokarin da yake yi
- Tsohon Shugaban Kasa Abdussalami ya yabawa El-Rufai na Kaduna
- Janar Abubakar yace ya ga ana ta aikin gyara makarantu a fadin Jihar
Labari ya iso mana daga Hadiman Gwamnan Kaduna cewa a karshen makon nan ne tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin Soji Janar Abdussalam Abubakar ya jinjinawa kokarin da Malam Nasir El-Rufai yake yi a fadin Jihar Kaduna.
Janar Abdussalami Abubakar mai ritaya yayi wannan jawabi ne lokacin da ya halarci wani taro na Kungiyar ZEDA da ke kokarin bunkasa ilmi a Garin Zaria. An yi taron ne da don bikin murnar cikar kungiyar 25 kaf da kafuwa.
KU KARANTA: PDP za ta karbi mulki a hannun APC inji tsohon Gwamnan Kaduna
Tsohon Shugaban kasar yace a lokacin da ya zo Zaria a mota tun daga Garin Jos zuwa Kano da kuma Kano zuwa Zaria ya ga manyan ayyukan da Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin El-Rufai ta ke yi a Garuruwa da Kauyuka da dama.
Abdussalami Abubakar ya yabawa yadda ake gyara makarantu a Jihar inda ya nemi sauran Gwamnonin Kasar su yi koyi da Gwamnan na Kaduna. A taron dai Gwamnan ya bayyana kokarin da yake yi na dawo da martabar ilmi a Jihar Kaduna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng