An yi wa El-Rufai raddi kan maganar rashin makarantun ‘Yan kasuwa a Amurka
- Gwamna Nasir El-Rufai yace babu makarantun ‘Yan kasuwa a Kasar Amurka
- Wata da ke Amurka ta ce wannan ba gaskiya bane don kuwa can ta kai yaron ta
- Bayan bincike mun gano cewa kusan dai akwai karya a kalaman na Gwamnan
Kwanan nan ne Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai yayi wata magana kan harkar ilmi wanda ba a sallama ma masa ba don kuwa kusan ta tabbata ba gaskiya bane. Kwanaki ma dai Gwamnan ya taba yin irin wannan inda aka gano karya ne.
Gwamnan a wani jawabi da ya fito daga bakin sa yace kaf Kasar Amurka ko da su ke kusan sun fi kowa bin tsarin guruguzu babu makarantar Firamare ta ‘Yan kasuwa. A cewar Gwamnan makarantun Firamare a Amurka duk na Gwamnati ne.
KU KARANTA: Ministan Shugaba Buhari zai garzaya Kotu da 'yan kasuwa
Gwamnan yayi wannan jawabi ne lokacin da ake wani taro na Kungiyar ZEDA a Garin Zaria game da yunkurin da su ke yi na gyara harkar ilmi. Sai dai jim kadan bayan yayi wannan jawabi wata ‘Yar jarida a Amurka Jamila Fagge tayi masa raddi.
Fagge wanda ta ke aiki a Gidan Rediyon VOA na Amurka ta bayyana cewa a Maryland kurum akwai makarantun Firamare 847 wanda duk na ‘yan kasuwa ne kuma nan ta ke kai yaron ta. Jihar Maryland dai tana cikin mafi kankanta a kaf Amurka.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng