Matashin da ya auri kanwar sa ya saduda, ya saki auren bayan matsin lamba

Matashin da ya auri kanwar sa ya saduda, ya saki auren bayan matsin lamba

- A kwanakin baya ne wani matsahi ya bayyanawa duniya aurensa da 'yar uwar sa ciki daya a dandalin sada zumunta

- Matashin ya sha suka a wurin jama'a har ta kai ga kungiyar kiristoci ta katolika ta yi barazanar kashe auren tare da tsarkake kauyen da aka daura auren

- Yanzu dai matashin, Chiadoki Ezeibekwe, ya bayyana hakura da auren 'yar uwar ta sa

Al'ummar kauyen Agba dake garin Ekwulobia ta karamar hukumar Aguata a jihar Anambra sun shiga rudani bayan wani matashi, Chiadoki; mai shekaru 25, ya bayyana auren 'yar uwar sa ciki daya mai shekaru 17.

Bayyana hakan keda wuya matsahin ya shiga bakin duniya har ta kai ga shugaban addinin Kirista mabiya darikar Katolika sun yi barazanar raba auren tare da tsarkake kauyen da aka daura auren.

Matashin da ya auri kanwar sa ya saduda, ya saki auren bayan matsin lamba
Matashin da kanwar sa da ya aura

Saidai matashin ya fito fili a yau lahadi ya bayyana cewar ya hakura da auren. Jaridar Sun ta rawaito cewar matashin ya bayyana hakan ne a bainar jama'a yayin halartar wani taro a wata makarantar sakandire dake karamar hukumar Isuofia.

Tuni dai Rabaran Igunatus Onwuatuegwu, ya saka ranar 24 ga watan Maris a matsayin ranar da zasu raba auren 'yan uwan junan.

DUBA WANNAN: Duk da dadewar 'ya'yanta a kan mulkin Najeriya, har yanzu Arewa ce kan gaba a talauci - Rabaran Kukah

Auren 'yan uwan ya zowa mazauna kauyen a matsayin abin mamaki bayan kafewar da matasan su ka yi cewar Allah ne ya yi ma su izinar cewar su auri junansu, a saboda haka ba su ga wani abin laifi cikin yin hakan ba.

Da yake bayyana hakura da auren nasu, matashin, Chiadi; kamar yadda aka fi kiransa, ya ce "duk da kasancewar aurenmu umarnin ubangiji ne, mun hakura da shi. Mun daina ma zancen auren kwata-kwata, zamu zuba ido mu ga abinda Allah ya yi mana tanadi a gaba, dama bamu yi nisa cikin auren ba domin ko sadaki ban biya ba kuma ba a yi shagalin biki ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng