Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci bikin diyar mataimakin sa Osinbajo a garin Abuja
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidan sa Aisha, suka halarci liyafar bikin Oludamola Osinbajo, diyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma angonta Oluseun Bakare a garin Abuja.
An daura wannan aure ne a tsakanin Damilola da Seun Bakare, da ga attajirar nan Bola Shagaya, a cibiyar addinin kirista ta kasa wato Natinaol Christian Centre dake babban birnin kasar nan na Abuja.
KARANTA KUMA: Rayukan da na salwantar sun haura 100 - Ade Lawyer
Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne aka yi bikin al'ada na baikon diyar Osinbajo a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng