Makiyaya sun kashe dakarun Soji 4 a wani artabun jihar Filato
Kamar yadda shafin jaridar Sahara Reporters ya ruwaito, 'yan ta'addan makiyaya na Fulani sun kashe dakarun soji hudu da safiyar ranar Larabar da ta gabata tare da da raunata dama a garin Miango na jihar Filato.
Rahotanni daga hukumar sojin sun bayyana manema labarai na Sahara Reporters cewa, wannan tsautsayi ya riski dakarun sojin ne a yayin da suke kan hanyar su ta rakiyar kwamandan Bataliyyar su.
Daya daga cikin dakarun sojin da ya ziyarci abokin aikin sa, Corporal Maidugu dake jinya a gadon asibitin Maxwell Khobe Catonment, ya bayyana cewa ajali ya katse ma sa hanzari sakamakon raunukan harsashi na bindiga.
KARANTA KUMA: Sirrika 5 da jan Wake ya kunsa ga lafiyar dan Adam
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar WAEC ta sauya jadawalin jarrabawar bana ta shekarar 2018 domin bayar da sarari ga musulmai wajen gudanar da ibandun su na sallar Juma'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng