Kungiya ta yi kira ga gwamnati ta mayar makarantar Dapchi ta jeka-ka-dawo

Kungiya ta yi kira ga gwamnati ta mayar makarantar Dapchi ta jeka-ka-dawo

Wata kungiyar mabiyya addinin Kirista da ke jihar Neja ta shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da makarantun kwana, musamman na mata da ke yankunnan arewa maso gabashin kasar nan zuwa na jeka-ka-dawo.

Hakazalika, kungiyar tayi kira ga al'umma su kafa kungiyoyin sintiri a unguwannin su don kare kansu daga kallubalen tsaro da ake fama dashi a yankin.

Kungiyar ta tayi wannan bayannan ne yayin da ta ziyarci iyallan wadanda aka sace musu yara daga makarntar sakandire na kimiyya da ke Dapchi a jihar Yobe.

Kungiya tayi kira ga gwamnati ta mayar makarantar Dapchi ta jeka-ka-dawo
Kungiya tayi kira ga gwamnati ta mayar makarantar Dapchi ta jeka-ka-dawo

A cikin kwanakin nan, Kungiyoyi da dama suna ta kiraye-kiraye ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki mataki kan halin rashin tsaron da ke addabar yankin ciki har da majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA: An damke wani mutum da ya yi wa diyar sa 'yar shekaru 14 ciki

Kungiyar na Kirista tana ganin canja makarantun kwanan zuwa na jeka-ka-dawo zai rage afkuwar sace matan da akeyi. Mayakan kungiyar ta Boko Haram sun sace matan ne a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018

Tun wannan lokaci gwamnati ta harzaka wajen nemo yan matan har ma zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya. Shugabanin hukumomin tsaro na kasar ma duk sun isa yankin na arewa maso gabas don tsananta neman yan matan.

Shugabanin hukumomin tsaron da suka koma yankin sun hada da shugaban jami'an tsaro, Janar Abayomi Olonisakin, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, shugaban sojin kasa, Janar Tukur Buratai.

Saura sun hada da shuguban yan sandan farin kaya na DSS, shugaban sojin sama na kasa, Air Marshal Sadique Abubakar da kuma mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164