Diya ta na sha'awar sarautar Kano idan na gama, inji Sarki Sanusi
- Sarki Muhammadu Sanusi II dai bai bayyyana sunan diyar nasa da ke son yin sarautar garin na Kano ba
- Ya kuma jadada cewa har yanzu ba'a gano zunzurutun kudi $20 billiyan da suka bace ba kafin a dakatar dashi a matsayin gwamnan bankin kasa
- Wani malamin addinin musulunci ya yi korafi kan auren diyar Ganduje da dan gwamna Ajimobi
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa daya daga cikin 'ya'yan sa mata tana son ta gaji sarautar birnin na Kano bayan ya gama mulkin sa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanusi ya furta wannan zancen yayin da ya ke wata hira da jaridar Financial Times a fadar sa a da ke birnin na Kano.
"Diya ta tana son tayi sarautar Kano bayan na gama kuma bata ji dadi ba kan yadda har yanzu ban zabi mace ba a majalisar zartarwa na masarautar Kano," inji Sarki Sanusi.
Sai dai Sarkin ya kame daga bayyana suna diyar tasa da ke son gadon sarautar na jihar Kano bayan ya kammala.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun kori wakilan Kwankwaso a wurin auren diyar Dangote
Da aka tambaye Sarkin game da yiwuwan hakan, Sarkin ya amsa da cewa sai dai jikan sa ko kuma jikan-jikansa ne zatayi sarautar amma ba diyar sa ba.
Sarkin ya cigaba da cewa ba abu ne da zai dauki lokaci mai tsawo sosai kafin al'umma ta karkata zuwa ga sabbon abu. Kuma akwai kaluballe sosai ga shugaba wajen tabbatar da al'addu da al'umma suka tashi a kai da kuma rungumar zamani.
Hakazalika, wani shahararen malamin addinin musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya yi korafi kan daurin auren diyar Ganduje da gwamna Ajimobi inda ya bayyana cewa abin kunya ne ga musulunci da arewacin Najeriya.
Legit.ng ta gano cewa Gumi ya gargadi al'umma game da fushin Allah inda ya bayyana rikicin Borno a matsayin sakamakon sabon Allah kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng