Sanata Kwankwaso ya bayar da agajin Buhunan shinkafa 1200 a jihar Zamfara
Mai martaba Sarkin Zamfaran Zurmi, Alhaji Abubakar Atiku Muhammad, ya jagoranci rabon tallafi na gudummuwar buhunan shinkafa 1200 da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar ga iyalan wadanda harin 'yan bindiga ya afkawa a makonnin da suka shude.
Tsohon gwamnan ya bayar da tallafin buhu 1200 na shinkafar ne ga iyalai da kuma 'yan uwan wadanda ibtila'i ya afkawa dake kauyen Birane na karamar hukumar Zurmi.
A yayin haka kuma kwamishina mai kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya, Sa'adiya Umar Faruk, ta bayar da gudummuwar kudi na Naira miliyan daya hadi da tallafin gero, wake, masara da kuma gishiri na kimanin buhuna 268, baya ga sabulan wanka, injinan ban ruwa da sauran kayayyaki na more rayuwa.
An kasafta wannan tallafi a ranar Alhamis din da ta gabata, inda aka baiwa magada wadanda suka rasu buhunan shinkafa 22, masara 1, wake 1, gero 1 da kuma zunzurutun kudi na Naira dubu goma.
Legit.ng ta fahimci cewa, an bayar kasafin buhunan shinkafa bakwai, gero 1, masara 1 sai kuma rabin buhun wake da Naira dubu goma ga wadanda harin ya raunata.
KARANTA KUMA: Duk barayin gwamnati sai sun fuskanci fushin doka - Magu
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kaso ya kuma hadar har da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukan su a hare-haren 'yan bindiga da suka afku a shekarun baya.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar IOM tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya sun yakito bakin haure 152 na Najeriya daga kasar Libya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng