Wani Hakimi ya kashe daya daga cikin wadanda su ka yi kokarin garkuwa da shi, ya raunata biyu
Hakimin garin Mayo Selbe a karamar hukumar Gashaka, jihar Taraba, ya bawa wasu da su kayi kokarin garkuwa da shi mamaki.
Hakimin, Jauro Hammangabdo, ya kashe daya tare da raunata biyu daga cikin wadanda su ka hauro fadar sa tare da kokarin sace shi.
Masu garkuwar, su tara, sun shiga fadar Hakimin tare da kokarin sace shi daga dakinsa na bacci.
Saidai basaraken ya tirje yayin da su ke kokarin tafiya da shi, har ta kai ga tsohon tsimi ya motsa ya saka hakimin dauko wata takobinsa tare da soke daya daga cikin 'yan ta'addar.
Ganin haka ya saka ragowar rantawa cikin na kare tare da barin bindigoginsu.
DUBA WANNAN: Sabon rikici tsakanin makiyaya da manoma a Filato: An kashe sojoji biyu
Mataimakin gwamnan jihar, Haruna Manu, ya jajantawa dan uwa ga hakimin bisa afkuwar harin da aka kaiwa, Hammangabdo, tare da jinjinawa namijin kokarin da ya yi.
Kazalika shugaban karamar hukumar Gashaka, Mohammed Gayam, ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) afkuwar lamarin tare da bayyana cewar ya ziyarci hakimi Hammangabdo kuma yana samun kulawa sakamakon rauni da ya samu yayin gwabzawa da 'yan ta'addar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng