Guguwar Buhari baza ta yi aiki ba zaben 2019 – Gaddama
- Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Bonro ya ce guguwar Buhari bazata kara aiki ba
- Gaddama ya ce gazar gwamnatin Buhari yasa mutane sun canza tunanin su akan sa
Zanna Gaddama Mustapha, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Borno yace, guguwar Buhari bazata kara aiki ba a zabe mai zuwa saboda gazawar gwamnatin sa.
Zanna, ya bayyana hakane a wata hira da yayi da ‘yan jaridar Daily Trust a birnin Maidugiri.
"Mutane sunyi tunanin cewa idan Buhari ya zo mulki, baza a kara jin motsi mayakan kungiyar Boko Haram ba kuma za su iya komawa gidajen su.
“Sunyi tunanin cewa a mulkin Buhari, buhun shinkafa zai dawo N3,000 daga N8,500, kuma za a 'karin albashi, sannan darajar kudin kasar zai 'karu.
KU KARANTA : Kungiyar Izala ta fara gudanar da gasar kacici-kacici karo na farko a jihar Kaduna
“Wannan shine tunanin ‘yan Najeriya a lokacin da suka fito 'kwan su da 'kwarkwatar su suka zabe Buhari.
“Rashin aikin yi a ko'ina a fadin kasar, da tsadar rayuwa yasa mutanen kasar canza tunanin su akan sa.
“Mutanen Maiduguri sun zama mabarata, idan dan Maidudguri ya samu abincin safiya bai da tabbacin kara samun na rana ko na dare kuma,” Inji Zanna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng