Alheri danko: Daliban Kwankwaso da su ka yi aure sun sanyawa diyar su sunan matar sa
Sulaiman da Maijidda na daga cikin dumbin matasa 'yan asalin jihar Kano da tsohon gwamna Rabi'u Kwankwaso ya tura karatu kasar waje kuma su ka yi aure bayan kammala karatunsu a kasar Uganda.
Yanzu dai Allah ya albarkace su da haihuwar diya mace kuma sun sanya ma ta sunan uwargidan sanata Kwankwaso, Salamatu Rabi'u Musa Kwankwaso. Magoya bayan kwankwaso sun yiwa jaririyar marhabun da shigowa ayarin kwankwasiyya.
Ga hotunan iyayen da kuma kyayawan diyar a kasa sanya da kayan sanyi masu launukan fari da ja kamar dai irin shigar da Dr Rabiu Musa kwankwaso da magoya bayansa sukeyi.
KU KARANTA: Sauya sheka: Mutane fiye da 2000 sun bar APC zuwa PDP a jihar Kano
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng