Duniyar Kimiyya tayi babban rashin FArfesa a daren jiya: Farfesa Stephen Hawkins

Duniyar Kimiyya tayi babban rashin FArfesa a daren jiya: Farfesa Stephen Hawkins

- Farfesa Hawkins ya kara shekaru 55 a duniya bayan da likitoci suka bashi shekaru biyu kacal

- Ya rasa aiki da gabban jikinsa, ba kuma ya iya magana sai ta Kwamfiyuta

- An yi makokinsa a fadin duniya

Duniyar Kimiyya tayi babban rashin FArfesa a daren jiya: Farfesa Stephen Hawkins
Duniyar Kimiyya tayi babban rashin FArfesa a daren jiya: Farfesa Stephen Hawkins

Duniyar Ilimin Boko da masoya kimiyya na fadin duniya na makokin babban hazikin ilimin kimiyyar science wanda ya rasu a daren jiya bayan ya shaffe shekaru 76 a duniya.

Stephen Hawkin, ya rasu bayan da ya shafe shekaru 55 yana jinya, saboda wata cutar gabbai da ta kama sassan jikinshi, cuta da ta lalata komai banda kwakwalwarsa, wadda ake kira motor-neuron disease., ya rasu ya bar 'ya'ya da mata daya.

An sami ilimai dubbai ta hannunsa, musamman bincike da yayi kan sammai da kwayar zarra, bincike da ya kawo duniya halin da take ciki yanzu, na abubuwa da kuke gani kullum da ma magunguna da ake warkar da cutuka dasu.

DUBA WANNAN: An janye yajin aikin manyan malaman jami'a

Ya daina magana tun yana saurayi, amma hakan bai hana shi ci gaba da binciken kimiyya ba, inda yake amani da wata kwamfiyuta da take magana a madadinsa, bayan ta karanta idonsa da kwakwalwarsa ta san me yake son fadi.

Hawkins ya mutu baya bin kowanne addini, inda ya kira addinai a matsayin chamfi da kuma cewarsa illar jahilci bata kai illar karamin sani ba, da ma kiran masu tsoron mutuwa da cewa su kamar yara ne masu tsoron zama a duhu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng