IG na ‘Yan Sanda yayi bakam bayan ya sa labule da Shugaban kasa

IG na ‘Yan Sanda yayi bakam bayan ya sa labule da Shugaban kasa

- Sufetan ‘Yan Sanda ya amsa kiran Shugaban kasa Buhari jiya

- An zargi IG na ‘Yan Sanda da sabawa Shugaban kasar a baya

- Shugaba Buhari ya nemi IGP Ibrahim K. Idris da ya kare kan sa

Mun samu labarin yadda aka kare bayan Sufeta Janar watau IG na Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim K. Idris ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. An dai rasa gane abin da aka tattauna a fadar Shugaban kasar.

IG na ‘Yan Sanda yayi bakam bayan ya sa labule da Shugaban kasa

Sufetan ‘Yan Sanda ya gana da Shugaba Buhari a Aso Villa

Idan ba ku manta ba jiya da sassafe Sufetan ‘Yan Sandan ya je fadar Shugaban kasa domin amsa wani sammaci da Shugaba Buhari yayi masa bisa zargin sa na bijirewa umarnin Shugaban kasar da yace ya koma Jihar Benuwe kwanaki.

KU KARANTA: GwamnanJihar Jigawa ya sa an yi ram da 'Dan jarida

Mun samu labari daga Vanguard cewa Shugaban kasar ya gana da IGP Ibrahim Idris a ofishin sa inda su ka sa labule na kusan rabin sa’a. Ko da aka gama zaman, Sufetan ‘Yan sandan yayi gum ne bai cewa ‘Yan jaridar da ke Aso Villa komai ba.

Gwamnan Jihar Benuwe wanda su ke ‘yar tsama da Sufetan ‘Yan Sandan ya fadawa Shugaban kasa cewa IG bai bi umarnin sa ba wanda shi kuwa yace bai sani ba. Ko da aka tuntubi fadar Shugaban kasar game da zaman ba tace uffan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel