Ana zaman dar-dar a Kuros-Riba bayan an sace Matar ‘Dan Majalisa

Ana zaman dar-dar a Kuros-Riba bayan an sace Matar ‘Dan Majalisa

- An kuma sace Iyalin wani ‘Dan Majalisa a cikin Jihar Kuros-Ribas

- Masu garkuwa da mutane ne ake zargi da yin wannan danyen aiki

- Jami’an ‘Yan Sanda sun toshe hanyoyin shiga da fita domin gano ta

Labari ya zo mana daga Daily Post cewa an sace matar wani ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Kuros-Riba wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai a Majalisar lokacin da ta kokarin dawowa daga ziyarar tsohuwar ta a Garin Ikot Ishie.

Ana zargin dai cewa masu garkuwa da mutane ne su ka sace Misis Nseobong Nelson Ofem a Ranar Alhamis da yamma lokacin da ta ke kokarin shiga mota. Kamar yadda labari ya zo mana dama masu garkuwa da mutanen su na dakon ta.

KU KARANTA: An kama masu satar amsa a JAMB kuma za a garzaya da su Kotu

Wadanda su ka sace matar ‘Dan Majalisar dai sun ajiye motar su ne a bayan motar ta kirar jif inda su ka yi wuf su ka yi gaba da ita su ka tsere kafin wadanda ke rakiyar ta su iya yin wani abu. Yanzu dai an ja matar zuwa wani boyayyen wuri.

Ko da aka tuntube wadanda su ka sace matar, sun tabbatar da cewa ta na hannun su amma ba su nemi a biya wani abu ba don su sake ta ba. Irene Ugbo wanda ke magana a madadin Jam’an ‘Yan Sanda sun ce za su gano iyalin ‘Dan Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng