Ihu bayan hari: Da mun san za’a sheƙe aya kamar yadda aka yi a bikin diyar Ganduje, da mun kama su – Hisbah

Ihu bayan hari: Da mun san za’a sheƙe aya kamar yadda aka yi a bikin diyar Ganduje, da mun kama su – Hisbah

Babban mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Yakubu Maigida Kachako ya bayyana cewa hukumar Hisbah bata da masaniyar irin badalar da aka shirya a bikin diyar Ganduje.

Dakta Kachako ya bayyana hake ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labaru a babban ofishin Hisbah na jihar Kano, inda yan jaridun suka je jin ta bakin hukumar, kamar yadda shugabanta Aminu Daurawa ya bukaci duk mai son jin matsayin Hisbah game da aure ya biyo su ofis.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa gwamnan jigawa ya sa Yansanda su kamo masa wani ɗan jarida

Rariya ta ruwaito Kachako yana fadin da ace hukumar ta samu labarin irin batancin da aka shirya a bikin, tabbas da ta tur jami’anta sun tarwatsa taron tare da kamo duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin harkar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban na Hisbah ya cigaba da fadin lallai da sun yi kame a wajen bikin saboda tun da suka fara aiki, gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje baya musu katsalandan a aikinsu.

Da yake karin haske, Maigida Kachako yace alamu sun suna shi kansa gwamna Ganduje bashi da masaniya game da irin badalar da yan biki suka aikata a bikin diyar tasa ba, don kuwa da ya sani da bai bari hakan ta faru ba.

Kimanin sati biyu kenan da suka gabata ne dai aka daura auren Fatima Ganduje da sahibinta Idris Ajimobi a birnin Kano akan sadaki naira 50,000, auren da ya sha suka sakamakon irin hotunan Amarya da Ango da suka dinga yawo a shafukan yanar gizo marasa kima.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng