Soja ta kashe wata mata a garin Aba

Soja ta kashe wata mata a garin Aba

- An shiga rudani yayin da soja ta kashe wata mata a garin Aba

- Rundunar soji sun tafi da gawar matar da aka kashe dan gudanar da bincike

Ana zargin wata soja dake aiki a makarantar, Ngwa High School, karkashin rundunar, Operation Base (FOB) wanda ba a bayyana sunan ta ba da kashe wata mata a garin Aba dake jihar Enugu.

Legit.ng ta samu rahoton cewa matan da aka kashe tasha ruwan harsasai yayin da rikici ya barke tsakanin wata soja da wani ma tukin amalanke.

Wani wanda abun ya faru a gaban shi, ya fadawa manema labaru cewa, al’amarin ya faru ne yayin da wata soja ta umarci wani mai tuka amalanke ya canza hanyar da ya biyo, ya bi wata hanyar.

Soja ta kashe wata mata a garin Aba

Soja ta kashe wata mata a garin Aba

“Shi kuma mai amalaken yayi kunnen uwar shegu, ya cigaba da tafiyar sa duk da umarnin da ta ba shi,

KU KARANTA : Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya

“Da tayi kokarin hana shi bin hanyar, sai ya fusata ya fara kokuwa da ita, har nemi ya kwace mata bindiga daganan sai ta yi harbe wanda ya samu wata mata da ake zargin tana da tabin hankali.

Rudunar sojoji sun tafi da mutumin tare da gawar matar da aka harbe dan gudanar da bincike.

Har zuwa yanzu rundunar soji na 144 Battalion basu fitar da wani jawabi game da wannan al’amari ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel