To fa Nesa ta zo kusa: Kasashen Larabawa sun bayyana birnin Kudus a matsayin birnin su na gado
- Kasashen tarayyar Larabawa ta ce daga yanzu birnin Kudus ya zama birnin ta na gado
- Kungiyar ta ce zata yi bikin tuna wa da wannan ranar a shekarar da za a shiga ta 2019
- Kwanakin baya ne dai kasar Amurka ta ce zata maida helkwatar jakadancin ta birnin Kudus din
Kamfanin dillacin labarai na kasar Falasdin WAFA ya bayyana cewa, kasashen tarrayar larabawa sun gudanar da biki a helkwatar kungiyar da ke birnin Alkahira na kasar Masar sakamakon tuna ranar birnin Kudus.
DUBA WANNAN: Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018
Shugaban Kungiyar raya kasar ta Kudus Halil Karraje Al-Rufa'i shine ya jagoranci zaman a inda yayi jawabin cewar, kungiyar tarayyar Larabawan ta amince da birnin Kudus ya zama birnita na Gado, sannan kuma ta ce zata gudanar da babban biki na tuna wannan ranar shekarar 2019.
Kwanakin baya ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana birnin Kudus a matsayin helkwatar jakadancin Amurka ta Isra'ila, yayin da hakan ya janyo cece-kuce a duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng