EFCC ta garkame asusun bankin wanda tayi wa Jonathan hidimar kamfe a 2015

EFCC ta garkame asusun bankin wanda tayi wa Jonathan hidimar kamfe a 2015

- EFCC na zargin tsohuwar Shugabar NSITF da karkatar da wasu kudi

- Ana zargin Olojeme da yin gaba da da wasu kudi har Naira Biliyan 68

- Hukumar ta rufe akawun din ta na banki sannan kuma an karbe gidaje

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta garkame asusun banki akalla 30 da kuma wasu gidaje kimanin hakan daga hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF.

EFCC ta garkame asusun bankin wanda tayi wa Jonathan hidimar kamfe a 2015
Magu ya gano wasu makudan dukiya wajen tsohuwar Shugabar NSITF

An samu wadannan makudan dukiya ne wajen Ngozi Olojeme wanda tayi wa Jonathan hidima a matsayin Mataimakiyar Darektar kudi wajen yakin neman zaben 2015. Yanzu haka dai an damke Darektan na NSITF da wasu Ma’aikata.

KU KARANTA: EFCC na zargin yaron wani tsohon Minista da laifin sata

Ana zargin Ngozi Olojeme wanda ta rike Ma’aikatar ta NSITF daga 2009 zuwa 2015 da karkatar da kusan Dala Miliyan 50 wanda ya kai Naira Biliyan 68. Wannan mata tana da akawun sama da 20 a Bankin First Bank da kuma GTB ban da tarin dukiya.

Yanzu dai ana ta bincike inda wannan Baiwar Allah ta musa cewa akwai hannun ta wajen satar wadannan kudi. An dai karbe gidaje da dama a Abuja da manyan Garuruwa irin su Bayelsa da Delta da kuma manyan filaye daga hannun ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel