Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi

Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi

- Dakta Ahmad Gumi, yayi Allah wadai da irin badalar da aka yi a bukin diyar gwamnan jihar Kano

- Dakta Ahmed Gumi ya soki hukumar Hisban jihar Kano saboda rashin daukan mataki akan badalar da aka yi a lokacin bukin diyar Ganduje

Dan gidan marigayi, Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Dakta Ahmad Gumi, yayi Allah wadai da irin badalar da aka yi a bukin diyar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje.

Dakta Ahmed Gumi, ya ce har idan kanawa basu shiga taitayin su ba, azabar Allah zai iya fado musu ta sanadiyar haka saboda yin haka tashin hankali ga addinin musulunci.

Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi
Bukin diyar Ganduje, tashin hankali ne ga musulunci da tarbiyyar ‘ya’yan mu – Sheikh Gumi

Shehin Mallamin, ya bayyan haka ne karatun Dandalin Sunna da ya saba yi a kowani mako a masalacin Sultan Bello.

KU KARANTA : A Najeriyar mu: Yadda wani saurayi mai shekaru 23 ya auri kanwarsa mai shekaru 16

”Ku duba irin abin da akayi a Kano, Abin yana bani bakin ciki. ace diyar gwamnan ta fito tana rungumar wani kato. Sannan kuma a garinne aka dakatar da wata ‘yar fim don ta rungume namiji. Toh ga diyar gwamnan ku ta runguma kenan yanzu za a halatta barin haka ya cigaba da faruwa zai lalata tarbiyar yaran mu.

”Sannan ina hukumr hisbah suke, shugabannin da muke sa wa kenan. Wallahi kunga yadda Allah ya maida garuruwa, to wallahi garin Kano suyi hankali, da wannan fasikancin Allah zai iya halaka garin Kano. Kunga yadda Maiduguri ta zama ," Inji shi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng