Birane 50 mafi hatsari a duniya
- Jerin birane guda hamsin wadanda suka fi ko ina hatsari a duniya
Hukumar tsaron rayukan al'umma da hadin gwiwar kotun manyan laifuka ta kasar Mexico sun bayyana birane 50 da suka fi hatsari a duniya a shekarar 2017.
DUBA WANNAN: Cutar mura mai karfi wacce zata iya sanadiyyar mutum milyan 300 su rasa ransu ta bulla a duniya
Daga cikin biranen 50, an bayyana cewar 42 suna Latin Amurka.
Dangane da kasashe, birane 17 na Brazil, 12 Mexico, 5 Venezuela, 3 Columbia, 2 Honduras sai kuma daddaya a Salvador, Porto Rico da Guatemala.
Birnin da ya fi ko wanne hatsari a duniya shine Los Cabos dake kasar Mexico inda a cikin shekarar 2017 a cikin kowane mutun dubu 10 ana kashe 112
Birnin na biyu a jerin birane masu hastari a duniya shine Caracas babban birnin Venezuela dake da wuraren bude ido inda a shekarar 2017 a cikin kowane mutun dubu 10 ana kashe 112.
Birni na uku shine Acapulco dake Mexico inda a cikin duk mutum dubu 10 ana kashe 106 a shekarar 2017.
Sai kuma birnin Natal inda ake kashe mutum 102 daga cikin dukkan dubu 10 a shekarar 2017
Sai kuma birnin Fortaleza inda kisar rayuwar dan adam ta karu da kaso 50 cikin dari
Birane goma da suka fi hatsari a duniya sun hada da:
Los Cabos (Mexico), Caracas (Venezuela), Acapulco (Mexico), Natal (Brazil), Tijuana (Mexico), La Paz (Mexico), Fortaleza (Brazil), Victoria (Mexico), Guayana (Venezuela) da kuma Belem (Brazil)
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng