Yawan al'umma ne babban abin da muke alfahari da shi a Kano - Ganduje

Yawan al'umma ne babban abin da muke alfahari da shi a Kano - Ganduje

- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa yawan al'umma yana da matukar amfani har idan al'ummar ta ginu kan sana'a da ilimi

- Gwamnan ya fadi hakan ne yayin da ya ziyarci kamfanin sarrafa motocci na Peugeot inda matasan Kano 150 ke koyan makamashin aiki

- Matasan da ke koyan aikin sun hada da maza guda 100 da kuma mata 50

A ranar Talata ne Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi dau alwashin amfani da dimbin al'ummar da Allah ya albarkaci Kano da shi don habbaka tattalin arzkin Jihar.

Ganduje ya yi wannan furucin ne a ranar Talata yayin da ya ziyarci matasa maza da mata 150 da gwamnatin jihar sa ta dauki bawa damar koyan aiki a kamfanin sarrafa motocci na Peugeot da ke garin Kaduna.

Ya kuma yi alkawarin bawa gwamnatin sa ba za ta bar mata a baya ba a duk harkokin cigaba da ake gudanarwa. Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa cikin matasan 150, guda 100 maza ne sannan 50 mata ne.

KU KARANTA: Yadda gawa ta farfado bayan likitoci sun tabbatar da ya mutu

"Yawan al'umma na iya zama matsala shi yasa muke daukan matakai don ganin yawan al'ummar su ta zama me amfani ta hanyar koyar da su sana'o'i.

"Muna koyar da ku sana'o'i ne ba don ku kadai ku amfana ba, muna fatan kuma za ku koyar da wasu." inji Gwamnan

Ya kuma kara da cewa zamanin da ake barin mata a baya wajen sana'o'i ya wuce, shiyasa gwamnatin sa ba ta kasa a gwiwa wajen tallafa wa matan.

Don hakan ne ma gwamnan ya ce gwamnatin sa ta kashe naira biliyan 5 don gina katafaren wurin koyar da sana'o'i saboda ilimin da dalibai ke samu a makarantu baya koyar da su dabarun sana'o'i da kasuwanci da za su iya yi bayan kamalla karatun.

A jawabin sa, Babban Direktan kamfanin ta PAN, Mr. Ibrahim Boyi ya ce wannan ne karo na biyu da suke koyar da matasa daga jihar ta Kano kuma za suyi iya kokarin su don ganin dukkan matasan sun koyi aikin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: