Kai dan ta'adda ne jahili makiyin jihar Kaduna – El-Rufai ga Shehu Sani

Kai dan ta'adda ne jahili makiyin jihar Kaduna – El-Rufai ga Shehu Sani

- Gwamnan jihar Kaduna, mallam Nasir El-Rufai ya caccaki sanata Shehu Sani

- Ya bayyana shi a matsayin makiyin jihar sannan kuma dan ta’adda

- El-Rufai ya sha alwashin daukar mataki akan sanatan

Rahotanni sun kawo cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yiwa sanatan dake wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani wankin babban bargo.

El-Rufai ya bayyana Shehu Sani a matsayin jahili wanda bai son ci gaban jihar Kaduna, sannan kuma cewa ya nunawa duniya cewa shi din dan ta’adda ne.

Hakan ya biyo bayan kin amincewa da Shehu Sani yayi kan yunkurin ciwo bashin dala miliyan 350 daga bankin duniya da jihar ke yunkurin yi.

El-Rufai ya yi wadannan furuci ne yayinda yake amsa tambayoyin manema labarai a wani shiri da gwamnatin jihar ta dauki nauyin gabatarwa, kan ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar.

Ya kuma jaddada cewa lokaci yayi daa Jama'ar Jihar Kaduna zasu bude idanuwa sosai domin gane masoyan su da kuma makiyan su, inda ya bayyana Shehu Sani a matsayin mai adawar gangan domin mayar da hannun agogo baya akan ayyukan cigaban jihar, da kuma kokarin cusa siyasa akan batun maganar ciwo bashin.

Ya sha alwashin cewa zai dauki duk matakin day a kamata gurin ganin Sanatan bai cimma manufarsa ba, saboda kamar yadda ya bayyana Shehu Sani bai san komai dangane da batun sarrafa kudi ko juyasu ba, abinda ya sani kawai shine a bashi ya kashe.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Arewa sun koka da Gwamnatin APC; sun ce Shugabanni sun yaudare su

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa duk abinda da gwamna El-Rufai ke ji da shi, ya tara ya samu, “Idan yaki yak enema, mun shirya ma babban yaki.”

The Cables ta ruwaito Sanatan ya bayyana haka ne bayan ganawa da kwamitin jin bahasi wanda uwar jam’iyyar APC ta aiko ta jihar Kaduna don jin bayanai daga dukkanin bangarorin jam’iyyar a jihar da basa ga maciji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng