Buhari na halartan bikin samun ‘yancin kasar Ghana a yau Litinin
- A yau kasar Ghana ta cika shekaru 61 da samun 'yanci kai
- Buhari ne kadai shugaban da gwamnatin kasar Ghana ta gayyata zuwa bikin cika shekaru 61 da samun yancin kai
A yau ne ake sa ran shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kama hanyar tafiyar sa zuwa birnin Accra na Ghana don halartar bikin cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai.
Babban hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fannin watsa labaru, Femi Adesina, ya bayyana haka inda yace Buhari ne kadai shugaban da aka gayyata daga wata kasa zuwa bikin.
Kuma, Buhari, ne kadai shugaban da aka zaba a matsayin bakon da zai gabatar da jawabi bayan shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya kammala nasa jawabin.
KU KARANTA : Fadar shugaban kasa tayi magana a kan satar 'yan matan Dapchi, takarar Buhari
Femi Adesina ce, shugaba Buhari, zai yi amfani da damar ziyarar wajen karfafa dankon zumunci da ke tsakanin kasashen biyu.
A cikin mutane da ake sa ran za su raka, shugaba Buhari, akwai Ministan harkokin waje, Goffre Onyama da mai ba wa shugaban kasa shawara a harkokin tsaro, Babagana Mongunu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng