Babu inda kananan yara suka kada zabe a Kano – INEC ta wanke Kano
- Kwamitin bincike na hukumar INEC ta ce babu inda kananan yara suka yi zabe a Kano
-INEC ta ce korafe-korafen da aka ta yi na cewa kananan yara sun kada a jihar Kano karya ce
Abubakar Nahuce, shugaban kwamitin bincike da hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) ta nada, dan binciken magudi da ake zargi an yi zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Kano, ya bayyana cewa babu inda kananan yara suka yi zabe a a jihar Kano sabanin korafe-korafen da ake ta yi a kwanakin baya na cewa kanana suna cikin wadanda suka yi zaben.
Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Juma’a lokacin da ya zanta da manema labaru a jihar Kano.
Abubakar ya ce ”Binciken da muka gudanar tun zuwan mu Kano, bai nuna tabbacin hakan ya faru ba. Mun tattauna da ‘yan jarida, kungiyoyin sa Ido, duk babu wanda ya iya tabbatar mana sahihancin wadannan korafe-korafe".
KU KARANTA : Dokar kashe masu yada kalaman batanci: Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi kaca-kaca da majalissar dattawa
Idan ba a manta ba, ana zargin hukumar zabe na Jihar Kano cewa ta bari yaran da basu kai yin zabe ba kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da akayi a Jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng