Shugaban Sanatocin Najeriya Bukola Saraki ya gamu da rotse a Jihar Kwara

Shugaban Sanatocin Najeriya Bukola Saraki ya gamu da rotse a Jihar Kwara

- Fusatattun masata sun kora Saraki da duwatsu daga cikin wani Gari

- Sanatan ya leka Kauyen ne domin ganawa da Sarkin da kuma yin jaje

- Sai dai Shugaban Majalisar bai ji dadin yadda ziyarar ta shi ta kare ba

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr. Bukola Saraki ya gamu da rotse a Jihar sa yayin da ya kai wata ziyara. Wannan abu ya faru ne a Garin Lafiagi da ke Karamar Hukumar Edu a cikin Jihar Kwara.

Shugaban Sanatocin Najeriya Bukola Saraki ya gamu da rotse a Jihar Kwara
Bukola Saraki bai ji dadi ba bayan da ya kai ziyara Jihar sa

Shugaban Majalisar kasar ya gana ne da Mai girma Sarkin Lafiagi, bayan nan ne kuma ya nemi ya kai ziyara gidan wasu Bayin Allah da ake zargi Sojojin da ke tare da Sanatan Yankin watau Shaba Lafiagi su ka kashe su kwanaki.

KU KARANTA: An soki Shugaba Buhari na zuwa biki maimakon jaje a Yankin Boko Haram

Wannan dai ya jawo rikici inda wasu matasa su ka fusata su ka rika kokarin dirkawa tsohon Gwamnan duwatsu wanda ta sa don dole ya tsere daga Garin. Wasu na zargin Saraki ya hana a binciki wanda su kayi wannan barna.

Jaridar Sahara Reporters ce ta bada wannan rahoto a jiya Asabar. Dama dai wasu Kungiyoyi sun fara kiran a dauki mataki kan wadannan mutane da aka kashe ba tare da hakki ba a Garin kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng