An kuma: Wani dalibi dan Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a ilimi a Ingila

An kuma: Wani dalibi dan Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a ilimi a Ingila

- Bashir Isa Dodo mataimakin malamin jami’a ne a jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina kuma dalibi a sashen kimiyya a jami’ar Brunel, Ingila

- Ya gano wata sabuwar na’ura ta Lissafi mai suna Optical Coherence Tomography (OCT), wanda zata iya raba hotuna a cikin ido zuwa sassa daba-daban

- Wanna ya sa aka bashi lambar yabo na Aiki a Takarda a taron BIO-IMAGING na shekara 2018 a kasar Portugal

An kuma: Wani dalibi dan Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a ilimi a Ingila
An kuma: Wani dalibi dan Najeriya ya taka muhimmiyar rawa a ilimi a Ingila

Majiyar da tayi fira da Bashir Isa Dodo, ya fada mata cewa babanshi tsohon alkali ne, mahaifyar shi kuma tsohuwar malamar makaranta ce, dukansu ‘yan jihar katsina ne. na fara yarinta ta a kaduna kafin muka dawo katsina in da na fara karatu a makarantar Ulul-Albab Science Secondary School Katsina a shekara ta 2000.

'Na fara karatun jami’a ne a jami’ar Umaru Musa Yar’adua katsina, in da daga bisani kuma na koma kasar Malaysia da karatu inda na gama karatu na a bangaren Sorftware Engineering a shekara ta 2011. Na kara karatu a jami’ar East London, UK inda na gama a shekara ta 2013'.

DUBA WANNAN: Za'a kwaci gonakin Turara a kudancin Afirka, a maidawa bakaken fatu

Na kasance mutun mai son bincike a kan abubuwa don sanin abun da zai faru a gaba. Har ila yau ina so inga na taimaka kuma na inganta basirar daliban da nake koyarwa. Na kuma samu karfin gwiwa ne daga iyayena da surukai na.

Gwamnatin Tarayya ta tallafa mani ta hannun makarantar koyarwar ilimi (TETFUND). Duk da cewa wasu abokan aiki da ni kaina an manta da al’amarin mu wanda sai dai mu muka daukar nauyin kan mu har zuwa karshen karatun.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng