Gobara ta lashe sama da shaguna 600 a kasuwar Bida
- Gobaran da ba'a san sababin ta ba ta kone sama da shaguna 600 a tsohuwar kasuwar garin Bida da ke jihar Neja
- Ma'aiatan kashe gobara, Yan sanda da jami'an hukumar tsaro na NSCDC sun isa kasuwar don kokarin kashe wutar da kuma samar da tsaro
- Shugaban karamar hukumar Bida, Mohammed Badugu ya mika jajen kana ya ce gwamnati za ta yi kokarin sake gina kasuwar cikin lokaci kalilan
Wata mumunnan gobara da ta afku a daren Alhamis ta kone sama da shanaguna 600 a tsohuwar kasuwar Bida da ke jihar Neja. Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta ruwaito cewa gobarar ta fara ci ne misalain karfe 8.30 na daren jiya kuma tayi sanadiyar asarar dukiyoyi da wasu kayayaki a tsohuwar kasuwan.
Wanda abin ya faru a idanun su sun ce Ma'aikatan kashe gobara na Bida da kuma Ma'aikatan kashe gobara na kwalejin Fasaha na Bida sun hallarci wurin amma basu samu damar ratsawa cikin kasuwar sosai ba saboda shagunan da ke faron kasuwar ma duk sun kama da wuta.
DUBA WANNAN: PDP ba ta da sauran kima a idanun 'yan Najeriya - El-Rufai
Har lokacin da ake rubuta wannan rahoton, ba'a gano musababin abin da ya tayar da gobarar ba.
Shugaban Karamar Hukumar Bida, Alhaji Mohammed Badugu ya shaida wa NAN cewa kasuwar dungurungun ta kone kurmus a dalilin gobarar.
Ya tabbatar da cewa ma'aikatan kashe gobara na Bida da kuma da Kwalejin Fasaha har ma da Yan sanda da jami'an hukumar tsaro na NSCDC duk sun kawo musu doki amma dai gobarar ta riga tayi illa sosai.
Bayan nuna damuwar sa kan faruwar gobarar, Bagudu ya ce karamar hukumar za tayi kokarin sake gina kasuwar nan ba da dadewa ba.
Kwamishinan Yan sanda na jihar, Mista Dibal Yakadi ya tabbatar da faruwar gobarar inda ya kara da cewa jami'an hukumar sun taimaka wajen ganin bata gari basuyi amfani da damar wajen sace kayayakin da ke kasuwar ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng