Yunwa ce ta adabe ni har na kai ga sata, wata mai juna biyu ta fadawa kotu

Yunwa ce ta adabe ni har na kai ga sata, wata mai juna biyu ta fadawa kotu

- An gurfanar da wata mai juna biyu a gaban kuliya bisa tuhumar ta da satan turare wanda ta ce yunwa ce ta adabe ta har ta kai ga satar

- Wanda ake tuhuma ta amsa laifin ta kuma ta roki kotu tayi mata sasauci wajen yanke hukunci

- Alkalin kotun ta sallame ta tare ta yi mata gargadi na cewa kotu ba za ta sake yi mata afuwa ba idan ta maimaita wani laifin

A ranar Alhamis ne wata kotun majisatare da ke Zone 2 a Abuja ta sallame wata mata mai juna biyu, Maryam Abbas, mai shekaru 20 bayan an gurfanar da ita gaban kotun bisa tuhumar ta da satar kwalbar turare daya da kudin sa ya kai N32,000.

Bayan an gurfanar da Abbas gaban kotun, ta amsa laifin ta kuma ta roki alfarma wajen kotu da ayi mata afuwa don bakar yunwar da ta adabe ta ne ya ingiza ta aikata satar.

Yunce ce ta sa ni sata, inji wata mai juna biyu da ta saci turare na N32,000
Yunce ce ta sa ni sata, inji wata mai juna biyu da ta saci turare na N32,000

Alkalin Kotun, Emenisi Ebiwari ta sallame ta bayan saurarar rokon neman afuwar da tayi.

DUBA WANNAN: Abin mamaki: Wai gawa ta aiko sako cikin laya daga barzahu a kasar Masar

Ebiwari ta gargade ta da kasance mai kyawun dabi'u da kuma barin sata da ma sauran ayyukan laifi masu kama da satar don idan har aka sake kawo ta gaban kotun, ba za'a sasauta mata ba.

Wanda ya shigar da karar, Adeniyi Oyeyemi ya shaidawa kotu cewa wani Ejikeme Omeja ne ya shigar da kara ofishin yan sanda a na Wuse Zone 5 a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Mai shigar da karar ya ce a ranar na 2 ga watan Fabrairun ne matar da tafi shagon wanda ya shigar da karar kuma ta sace turaren wanda daga baya aka gano shi bayan yan sanda sun gudanar da bincike.

Oyeyemi ya ce laifin ya ci karo da sashi 287 na Penal Code.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel