Siyasa: Kujerar Sanata Shehu Sani tana kara rawa a Kaduna

Siyasa: Kujerar Sanata Shehu Sani tana kara rawa a Kaduna

- Arc. Shamsu Giwa ya bayyana cewa zai nemi takarar Sanatan Kaduna

- Sai Sanatan Kaduna Kwamared Shehu Sani yayi da gaske a zaben 2019

- Tun tale-tale Shamsu Giwa yake tare da Shugaba Muhammadu Buhari

Mun samu labari a makon nan cewa wani ‘dan siyasa ya kara fitowa takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya. Ma’ana dai sai Sanatan Kaduna na tsakiya mai-ci Shehu Sani yayi da gaske a zabe mai zuwa.

Siyasa: Kujerar Sanata Shehu Sani tana kara rawa a Kaduna
Shamsu Giwa na neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya

KU KARANTA: APC ba ta san abin da ta ke yi ba inji Jigo a Jam'iyyar

Arc. Shamsu Shehu Giwa ya bayyana cewa yana harin Majalisar Dattawa a zaben 2019 a kuma karkashin Jam’iyyar APC mai mulki. Shamsu Giwa tsohon ‘Dan Jam’iyyar ANPP ne kafin a dunkule a Jam’iyyar APC.

Siyasa: Kujerar Sanata Shehu Sani tana kara rawa a Kaduna
Jama'a da dama na neman kujerar Kaduna ta tsakiya

‘Dan siyasar na iya kawowa Shehu Sani wanda yanzu haka dama kujerar sa ta na rawa wani sabon cikas. Wannan ne karon farko da Kwamared Shehu Sani ya fara zuwa Majalisa kuma ba su jituwa da Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai.

Shamsu Giwa ya taba fitowa takarar Shugaban karamar Hukumar Giwa amma bai yi nasara ba. A kwanakin baya dai kun ji cewa wasu na ta kokarin hurowa wani na hannun daman Gwamnan wuta watau Uba Sani ya fito takarar Sanatan Yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng