Sanatoci za su binciki yadda Gwamnan Kogi yayi katin zabe sau 2

Sanatoci za su binciki yadda Gwamnan Kogi yayi katin zabe sau 2

- Ana zargin Alhaji Yahaya Bello yana da katin zabe sama da guda daya

- Wannan ya sabawa doka kuma ba don yana Gwamna ana iya kama shi

- 'Yan Majalisa za su binciki yadda Gwannan na Kogi yayi rajista sau 2

Mun samu labari ba da dadewa ba cewa Majalisar Dattawa za ta binciki Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello game da zargin da ke kan sa na yin rajistar katin zabe fiye da sau daya wanda hakan haramun ne.

Sanatoci za su binciki yadda Gwamnan Kogi yayi katin zabe sau 2
Majalisa za ta binciki Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello

An nemi Kwamitin da ke kula da zabe na INEC a Majalisa ta duba zargin da ke kan Gwamnan na yin rajista da Hukumar zabe sau biyu. Sanatan Hassan Muhammed na Yobe ne ya kawo wannan kudiri a Majalisa yace ya kamata a duba lamarin.

KU KARANTA: An soki nade-naden Shugaban kasa Buhari

Sanatan na PDP yace hakan zai kawo gyara a harkar zabe na kasar. 'Dan Majalisar yake cewa ya kamata a san ta yadda Hukumar zabe ta ba Yahaya Bello damar rajista har sau biyu. Ba don yana kujerar Gwamna ba dai yanzu an kama sa.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yace gyara harkar zabe shi zai tafiyar da siyasar kasar lafiya don haka ya nemi kwamitin harkar zabe a Majalisar su duba wannan batu su kuma kawowa Majalisa rahoto bayan sun kammala aikin su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: