'Matsin tattalin arziki ya sanya nake fashi da makami'

'Matsin tattalin arziki ya sanya nake fashi da makami'

Rundunar 'yan sanda ta jihar Neja, tayi ram da wasu mutane biyu masu da makami, Shehu Buda da Bello Mallam, wadanda suka yi ikirarin sun sanya taguwar wannan ta'addanci ne a sakamakon matsi na tattalin arziki da kuma samar da aikin yi da gwamnati ta gaza.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan biyu sun shiga hannu ne a unguwar Talba dake karamar hukumar Bida da jihar Neja.

Wannan matasa biyu masu shekarun 20 da kuma 18, ba su baiwa hukuma wata wahala ba yayin da suka amsa laifin su ba tare da wata nadama da cewar zasu koma bakin aiki ne da zarar sun sauke hukuncin da aka zartar akan su.

Rahotanni da sanadin Northern City News sun bayyana cewa, wannan matasa sun yi amfani da adda da kuma katako wajen raunata wani mutum mai sunan Muhammad Muammad, inda suka suka yi yunkurin fyade masa diya bayan sun yashe mai kudade da dukiya ta kimanin N16, 400.

KARANTA KUMA: Wani simame na Boko Haram ya salwantar da rayukan Dakarun Soji 2 a jihar Borno

Matasan biyu dai sun ce babu wani abin yi a halin da ake fama da matsin tattalin arziki da sace-sace na barayin gwamnati face su ci gaba da sana'ar su ta fashi da makami.

Suke cewa, mutane da dama a kasar ba abinda face sata wadanda sun hadar har da manyan ma'aikatan gwamnati. Yunwa sai dibar karen mahaukaciya take yiwa mutane tare da sheka su Barzahu. Ba mu da wani zabi face sana'ar sata da fashi da makami.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana adadin kudaden man fetur da jam'iyyar PDP ta wawushe cikin shekaru 16 na mulkin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel