2019: Shugaba Buhari zai gana da gwamnonin APC

2019: Shugaba Buhari zai gana da gwamnonin APC

A daren yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai gana da gwamnonin jam'iyyar su ta APC a dakin taro na uwargidan sa dake fadar ta shugaban kasa a babban birnin kasar nan.

Kamfanin dillancin labari na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan ganawa zata zamto ci gaban ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasa da gwamnonin a mahaifar sa ta garin Daura a ranar asabar ta makon da ya gabata.

Shugaba Buhari tare da gwamnonin APC
Shugaba Buhari tare da gwamnonin APC

Shugaban kungiyar gwamnonin na APC, gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, shine ya shaidawa manema labarai wannan batu da cewa, babbar manufar ganawar su da shugaban kasa a garin Daura shine jajintawa tare da bayyana ta'aziyar su gare shi dangane da rashin 'yan uwan sa biyu a makonnin da suka gabata.

KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta duƙufa domin shirya maguɗin zaɓe a 2019 - Secondus

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa, manufar ganawar su ta daren yau ita ce gamsar da shugaba Buhari akan ya sake tsayawa takara a zaben 2019 mai gabatowa.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnonin sun halarci ganawa ta zaman majalisar tsaro da shugaba Buhari ya jagoranta a fadar sa ta Villa.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, wata mata ta yashe asusun ta na banki tare da yin bushasharta bayan samun labarin mutuwar ta shekaru biyar da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng