Mahara sun kashe mutum 6 a wani mummunan hari a kauyen Birnin Gwari, jihar Kaduna
- Mahara sun kashe mutum 6 a wani mummunan hari a kauyen Birnin Gwari, jihar Kaduna
- 'Yan bindigar dai ana kyautata zaton barayin shanu ne kuma sun yi ta harbe-harben bindiga a sama
- Daga bisani su fatattki mutanen kauyen duka
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga dadi fataken dare da ba san ko suwaye ba sun afkawa wani karamin kauye wanda ake kira da suna Kaguru dake a karamar hukumar Birnin Gwari, jihar Kaduna.
KU KARANTA: Sojoji sun ceto 'yan matan makarantar Dapchi
Kamar yadda muka samu dai, maharan sun samu nasarar kashe akalla mutane shidda mazauna kauyen.
Legit.ng ta samu cewa 'yan bindigar dai ana kyautata zaton barayin shanu ne kuma sun yi ta harbe-harben bindiga a sama kafin daga bisani su fatattki mutanen kauyen duka.
Daya daga cikin 'yan garin da lamarin ya auku a kan idon sa ya shaidawa majiyar mu cewa bayan 'yan kauyen duka sun tsere sai maharan suka rika shiga cikin gidajen su suna kwance dukkan shanun da suka mallaka suna tafiya da su.
A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurni ga sojoji da kuma 'yan sandan Najeriya da su gaggauta zuwa su zagaye makarantar 'yan matan nan ta kwana mallakin gwamnatin jihar Yobe da ke garin Dapchi da 'yan Boko Haram suka kai wa hari.
Haka zalika shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bayyana cewa ministan tsaron kasar zai jagoranci wata tawagar gwamnatin tarayya zuwa makarantar gobe don samun ainahin musabbabin faruwar lamarin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng