Karfin hali: wani mutum ya dambace da wani Maciji sa’annan ya cizge kanta da hakoransa
Rahotanni sun bayyana wani mutumin kasar Indiya, mai suna Sonelal ya cizge wuyar wani maciji daya sare shi, wanda likitoci suka bayyan basu taba ganin irin wannan lamari ba.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito lamarin ya faru ne karshen makon da ya gabata a garin Uttar Pradesh, inda aka garzaya da mutumin zuwa Asibiti cikin hanzari don gudun kada dafinsa ya kashe shi.
KU KARANTA:
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sonelal ya bayyana ma yan uwansa cewa yana cikin kiwon dabbobinsa ne sai kawai yaji sara, wanda hakan ya harzuka shi ya cafki wuyar macijin da hakorinsa, nan da nan ta cizge wuyar.
“Macijin ne ya fara sara ta, sai na yi wuf na cafke wuyansa, na cizge shi gabadaya, na kashe macijin, sa’nnan kuma na dawo da shi kauyenmu, a nan ma na yayyaga kansa.” Inji Sonelal.
Shi ma likitan da ya duba Sonelal, Sanjay Kumar yace yayi mamaki matuka ganin yadda mutumin ya sha duk da saran da macijin yayi masa. “Ban taba ganin irin wannan ba, amma mutumin na nan lafiya duk da saran macijin.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng