2019: Sanata Marafa yace idan ya ji babu kan-ta zai bar APC
- Sanata Kabiru Marafa yace idan aka hana sa tikiti zai bar APC
- Marafa yace ya ga APC ta Jihar sa na neman hana sa tutan 2019
- Ana samun rikicin siyasa tsakanin Marafa da Gwamnan Zamfara
Sanatan Jihar Zamfara ta tsakiya Kabiru Marafa ya bayyana cewa ya shirya barin Jam’iyyar APC mai mulki idan har ba su da niyyar ba sa tikitin tsayawa takara a zabe mai zuwa. Akwai ma wasu Sanatocin da ke da wannan shiri.
Sanata Kabiru Marafa a Ranar Talatar nan yace idan har APC ba za ta ba shi tuta a Jihar sa ba, to babu shakka zai tattara ya bi wata Jam’iyyar adawa a kasar idan har aka yi masa alkawarin tikitin takarar Gwamna ko Sanatan sa.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yaba da aikin Gwamna Bindow
Kabiru Marafa ya bayyana wannan ne a zaman Majalisa lokacin da ya ke sa baki kan kudirin da wani Takwaran sa daga Jihar Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya kawo. Sanatan yayi kira da a sa dokar ta-baci a Jihar Zamfara.
Sanatan yace sakacin Gwamnan na Zamfara Abdulaziz Yari ya bayyana a fili inda ya gaza tsare rayukan jama’a. Sanatan yace ya ga alamun ana neman hana sa tikitin takara a 2019 a Jihar sa saboda sukar Gwamnan da yake yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng