Zamu marawa Buhari baya idan ya sake takara a 2019 – Dattawan kudu maso gabas
- Kungiyar dattawa kudu maso gabas ta sha alwashin marawa shugaba Buhari baya a zabe mai zuwa
- Ta jadadda cewa gwamnatin APC tayi matukar kokari wajen yakar cin hanci da rashawa da kuma yaki da ta’addanci
- Har yanzu shugaba Buhari bai nuna ra’ayin sake takara ba
Kungiyar dattawa kudu maso gabas sunyi alkawari marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben shugabancin kasa na 2019 idan har ya yanke shawarar sake takara, inda suka ce gwamnatin APC tayi kokari sosai wajen yaki da rashawa da kuma yan ta’addan Boko Haram.
Shugaban kungiyar sannan kuma tsohon shugaban kungiyar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, Dr Dozie Ikedife ya fadawa masu kawo rahoto a jiya a Nnewi cewa shugabannin kudu maso gabas sun yanke shawarar ne a taronsu da sukayi a Enugu.
KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya yada hotunan chanji da ya zaba yayinda ya yaba ma shugaba Buhari
Ikedife ya bayyana cewa ba a sani ba tukuna ko shugaba Buhari zai sake takara, ya kara da cewa baza a janye shi daga matsayin ba tunda bai nuna ra’ayi ba tukuna.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa yayin da Asiwaju Bola Tinubu, Shugaban Jam'iyyar APC na Kasa, ya fara sasantawa tsakanin 'yan jam'iyyar, matar sa, Sanata Oluremi Tinubu, ta fito ta koka da yadda a ka wofintar da mijin ta bayan APC ta ci zaben 2015.
Sanatar ta fadi hakan da ta bayyana a wani shiri na bayyan ra'ayi da safiyar ranar Litini da tashar talabijin na 'Television Continental'. Ta koka da yadda a ka jakice shi a ka mayar da shi saniyar ware duk da irin gudummuwar da ya bayar don tabbatar da jam'iyyar ta ci zaben.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng