Hadimin gwamnan jihar Katsina ya kashe yarsa da mota
Abun bakin ciki ya faru a ranar Juma’a a jihar Katsina lokacin da mai ba Gwamna Aminu Masari shawarar na musamman akan al’amuran addini, Abdullahi Darma, ya take yarsa, A isha da mota bisa tsautsayi.
Majiyoyi sun kawo cewa hadimin gwamnan bai san yarinyar na bayan motan ba.
“Motan ya take yarinyar sannan a take ta mutu a wajen,” inji majiya nakusa da su.
Darma ya buga mummunan labarin a Facebook, wanda ya ja hankulan mutane wajen yi masa ta’aziyya, inda wasu da dama suke je gidansa domin yi masa ta’aziyya.
“Yan mintuna kadan da suka shige, Allah ya jarabceni. Ina juyawa da motana lokacin da na take ýata bisa kuskure sannan kuma ta mutu,” cewarsa a shafin Facebook.
KU KARANTA KUMA: Bashir Dodo yayi binciken da zai taimaki marasa lafiyar idanu
Darma yayi Magana a takaace a ranar Lahadi lokacin da majiyarmu ta nemi sanin yadda abun ya faru.
Ya bayyana al’amarin a matsayin “nufin Allah.”
A wani al'amari na daban, Legit.ng ta samu labarin cewa wani hazikin Matashi da ya fito daga Jihar Katsina yayi suna a Duniya inda ya kammala karatun sa na Digiri na uku watau PhD a wata Jami’ar kasar waje kwanan nan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng