Hukumar Mahajjatan Najeriya ta rage kujerun Jihar Kogi
- Masu niyyar sauke farali za su biya Miliyan daya da rabi a bana
- Ya zama dola ayi takardun lafiya da fasfo da katin zama dan kasa
- Nan da karshen watan gobe ne za a rufe biyan kudin jirgi a Kasar
Hukumar Alhazai ta Kasar nan ta raba kujeru 717 ga Jihar Kogi domin aikin hajjin bana. Hukumar jin dadi da kula da Alhazzai na Jihar Kogi ta bayyanawa ‘yan jarida wannan a makon nan. Kuma Dole ne masu niyya su tanadi takardu.
Sheikh Lukman Abdullah wanda shi ne Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Kogi ya bayyanawa ‘yan jarida cewa Hukumar NAHCON me kula da Mahajjatan Najeriya ta rage yawan kujerun da ta saba ba Jihar Kogi a bana.
KU KARANTA: Najeriya za ta fara fita da gangar danyen mai miliyan a kullum
Abdullah yake cewa a wannan shekarar, an warewa Jihar Kogi kujeru 717 ne yayin da a bara kuwa an ba Jihar kujeru sama da 830. Sheikh Abdullahi ya bayyana wannan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Garin Lokoja.
A cewar Shugaban Hukumar Alhazzan na Jihar, lokaci ne zai kawo masu cikas wajen shiryawa aikin na Hajjin bana. An dai bada nan da karshen watan uku a kamalla biyan kudin sauke faralin wanda yanzu ya kai Naira Miliyan daya da rabi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng