Kashi 20% na 'yan sanda ne ke aiki, sauran zaman dirshan suke - AIG
- Rundunan Yan Sandan Najeriya ta gano cewa galibin jami'an na ta basu tabuka aiki komai sai lalaci kawai
- An gano hakan ne sakamakon wani bincike da hedkwatan Rundunar na tarayya ta yi domin magance lalaci da kawar da gurbatattun jami'ai
- Mataimakin Sifeta Janar na Zone 5, Mista Rashid Akintunde ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai garin Yenagoa
Rundunar yan sandan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan yadda jami'an rundunar ke gudanar da ayyukan su. An bijiro da binciken ne domin gano ma'aikata cima zaune da kuma gurbatattun jami'ai cikin rundunar.
Mataimakin Sifeta Janar na yan sandan zone 5, Mista Rashid Akintunde ne ya bayar da sanarwa jiya a garin Yenagoa yayin da ya ke zagawa domin duba ma'aikatan rundunar da yadda suke gudanar da ayyukan su.
KU KARANTA: Wani tsohon Janar yace Obasanjo da Babangida basu da ta-ido, da suke iya wa Buhari gorin aiki
Ya ce binciken da hedkwatan rundunar ta gudanar ya nuna cewa kwatankwacin jami'ai kashi 20 cikin 100 ne ke gudanar da aikin su yadda ya kamata a duk fadin kasar nan.
Ya kuma ce a cikin kashi 20 din da ke aiki, galibin su sun tatare ne wajen gadin Attajirai, Shugabanin addini, Kamfanoni da sauran su.
Akintunde ya shawarci jami'an rundunar su dage wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata domin rundunar ba za ta lumunce wa lalaci da rashin kwarewa wajen aiki ba duk da cewa suna fama da karancin kayayakin aiki da ma jami'ai.
A jawabin sa, Kwamishan Yan Sanda na Jihar Bayelsa, Mista Don Awuwah ya mika godiyarsa kan ziyarar da mataimakin Sifeta Janar din ya kai musu.
Idan mai karatu bai manta ba, Legit.ng ta kawo wani rohoton inda mataimakin shugaba kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce yana goyon bayan bawa jihohi ikon kafa yan sanda na kansu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng