Dandalin Kannywood: Allah ya yiwa tsohon mijin Sadiya Gyale rasuwa

Dandalin Kannywood: Allah ya yiwa tsohon mijin Sadiya Gyale rasuwa

Rahotanni sun kawo cewa tsohon mijin shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Sadiya Gyale wato Alhaji Abubakar Muhammad ya amsa kiran mahallicin sa.

Marigayin ya amsa kiran Allah ne a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya a ranar Litinin 5 ga watan Fabrairu.

Shafin Rariya ta rahoto cewa Alhaji Abubakar, wanda ya kasance shahararren ɗan kasuwa, ya rasu sakamakon ciwon hawan jini da ya kama shi, kuma ya rasu jim kaɗan bayan an kai shi asibiti.

Majiyar ta ce ya je Istanbul ne harkar kasuwancin sa kamar yadda ya saba, to sai Allah Ya yi ƙarshen tafiyar kenan.

A cewar majiyar, an tsara cewa za a kawo gawar sa Abuja daga Turkiyya ɗin washegari, wato Talata.

Dandalin Kannywood: Allah ya yiwa tsohon mijin Sadiya Gyale rasuwa
Dandalin Kannywood: Allah ya yiwa tsohon mijin Sadiya Gyale rasuwa

Shi dai marigayin, an ɗaura auren sa da fitacciyar jaruma Sadiya Gyale a kan sadaki N50,000 a ranar 10 ga Afrilu, 2015 a Kano.

Auren ya ja hankalin jama'a sosai, musamman masoyan jarumar, domin Sadiya na daga cikin matan fim da aka zaƙu a ga ranar auren su.

Hakan ya sa bikin auren ya samu halartar ɗimbin ƙawayen ta.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai sha kaye idan har ya tsaya takara – Shahararren Fasto

Amaryar da ƙawayen ta 'yan fim sun yi bikin auren har na tsawon kwana uku, daga ranar 21 zuwa 24 ga watan Mayu. An yi dabdala a ranar farko a Gidan Ɗanhausa, da wani ɗakin taro da ke Bompai (inda aka yi taron kamu a rana ta biyu), da dina a wani ɗakin taro da ke Titin Minjibir duk a garin Kano, a rana ta uku.

To amma angon bai halarci ko ɗaya cikin shagulgulan bikin ba.

Hasali ma dai amaryar ba ta kai ga tarewa ba ya sake ta, wanda hakan ya zama abin takaici da ban-mamaki matuƙa.

Tun daga lokacin kuwa Sadiya ba ta ƙara shiga harkar fim ba, kuma ba ta samu yin wani auren ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel