Kasuwancin da wasu jaruman hausa ke yi bayan shirin fim
Zama guri ɗaya tsautsayi inji kifi domin kuwa a yau dandalin kannywood na shafin Legit.ng, ya kawo muku jerin wasu shahararrun 'yan shirin fim, da suke buga harkokin su na kasuwanci bayan sana'ar ta su da suka shahara akai.
Wannan shi yake bayyana cewa, fitattaun jaruman ba su dogara akan sana'ar shirin fim kaɗai ba, inda suke ci gaba da hada-hadar su ta kasuwanci a wasu bangoririn rayuwa domin cikar burikansu da buƙatu na yau da kullum.
KARANTA KUMA: Ababe 9 dake janyo warin baki tare da hanyoyin ƙaurace musu
Ga jerin fitattuun jaruman da suke buge harka a masana'antun sy bayan sharar fage da suke a shirin fim:
Hadiza Aliyu Gabon: Wannan jaruma tana daya daga cikin jarumai da suka goge a shirin fim, kuma tana buga harkokin ta na kasuwanci a sana'ar yiwa mata kwalliya. Gabon dai tana da gidan kwalliyar ne mai sunan Hadiza Gabon Beauty Salon a garin Kaduna.
Maryam Booth: Ko shakka babu, masu bibiyar shafukan sada zumunta zasu tabbatar da cewa, wannan jaruma itama ta shahara a fagen yiwa mata kwalliya, inda take da shagon ta mai sunan Maryam Booth Beauty Parlour and Collection a jalla babbar hausa wato garin Kano.
Rahma Sadau: Kamar dai a ce wannan jarumai suna gasa ne da junan su, domin kuwa ita jaruma Rahma Sadau tana da nata shagon kwalliyar mai sunan Sadau Beauty Lounge a garin Kadua, inda kuma take da mallakin kamfanin shirya-shirya fina-finai mai sunan Sadau Pictures wanda 'yan uwanta ke gudanar da harkokin sa.
Isa A. Isa: Wannan jarumi ya dade da shahara a shirya fina-finai domin kuwa ya kasance mai bada umarni a karan kansa. A halin yanzu dai, wannan jarumi shike da mallakin katafaren kamfanin tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare mai sunan I A I travel Agency, yna kuma da shagon sayar da kayan sawa mai sunan Queen Nabile Boutique baya ga kamfanin shirya fina-finai mai sunan I A I entertainment an d Film Production.
Hassan Giggs: Wannan jarumi ya shahara a fagen bayar da umarni wajen shirin fim, inda a halin yanzu yake da katafaren kamfanin ruwa na roba tare da lemun sha kala daban-daban domin kwance ishirwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng