Mutanen Jihar Neja sun yaba da Gwamnatin APC
- Mutanen Jihar Neja sun shana a Gwamnatin Buhari ta APC
- Yanzu haka akwai ayyuka birjik da ake yi a cikin fadin Jihar
- An kammala wasu hanyoyi yayin da ake shirin karasa wasu
Mutanen Neja sun amfana da Gwamnatin Jam’iyyar APC mai mulki ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda su kace ba su taba amfana da Gwamnati irin wannan ba. Daga cikin amfanin akwai wata tashar ruwa a Garin Baro da ake yi.
Yanzu haka dai akwai ayyuka da dama da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kai Jihar ta Neja musamman a sha’anin hanyoyi kamar yadda wani babban Ma'aikac a gidan Gwamnatin Jihar Neja ya bayyyana. Jihar dai na fama da matsalar titi a Yankin.
KU KARANTA: Za a ga karuwar wutar lantarki a Najeriya a 2018
Abdulbaki Ebbo yayi amfani da shafin sa na Tuwita ya zayyano wasu ayyuka da Gwamnatin APC ke yi a Jihar Neja a yanzu haka. Daga ciki dai akwai manyan hanyoyi kamar ta Garin Suleja zuwa Garin Minna da kuma ta Kontogoro zuwa Yauri.
Ebbo wanda aka fi sani da Nupenchi a shafin Tuwita yace Gwamnatin nan na shirin kammala aikin Makera zuwa Kontogora da kuma ta Katcha zuwa Baro. Akwai kuma hanyar Rijau da yanzu haka ana ta faman aiki da kuma wata gada a Garin Tatabu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng