Makiyaya zasu cigaba da mulkin Najeriya, haka Allah ya kaddara - Farfesa Labdo

Makiyaya zasu cigaba da mulkin Najeriya, haka Allah ya kaddara - Farfesa Labdo

- Farfesa Umar Muhammad Labdo ya ce ba'a yiwa makiyaya adalci a Najeriya duk da cewa doka ya basu kamar yadda kowane dan kasa ke da yancin

- Malamin Jami'an ya kuma ce tun kafin zuwan turawa makiyaya sun iya karatu da rubutu, hakan ne yasa nauyin jagorancin al'umma ya rataya a wuyan su

- Ya kuma ce a lokacin da turawa suka iso kasar, Makiyaya ne ke mulkar al'umma kuma hakan za ta cigaba har sai wasu sun wuce su wajen ilimi

Farfesa Umar Muhammad Labdo ya ce makiyaya ne ke mulkin al'umma tun fil zan kuma bisa ga dukkan alamu lamarin ba zata canja zani ba domin haka Allah ya kadara.

A wata hirar da ya yi da jaridar Punch, Malamin da ke koyarwa a Jami'ar Maitama Sule da ke Kano ya ce makiyaya ne suka yadda ilimi a kasar tun kafin zuwan turawa.

Makiyaya zasu cigaba da mulkin Najeriya, haka Allah ya kaddara - Farfesa Labdo
Makiyaya zasu cigaba da mulkin Najeriya, haka Allah ya kaddara - Farfesa Labdo

Farfesan kuma ya yi Allah wadai ta dokokin hana kiwo da wasu Jihohin Najeriya suka kafa, inda ya ce makiyaya na da yancin gudanar da harkokin rayuwarsu kamar kowane dan kasa.

KU KARANTA: Son kai ya kai Obasanjo yi wa Buhari gangamin taron dangi - Edwin Clark

Kamar yadda Labdo ya ce "Wanda sukafi ilimi ne ke mulkar al'umma, kuma makiyaya sun fi kowa ilimi don sune suka koyar da sauran al'umma rubutu da karatu kamar yadda tarihi ya nuna tun shekaru 300 - 500 a baya. Hakan ya sa nauyin jagorancin al'umma ya rataya a wuyan su, Allah ne ya kadara hakan amma na san idan wasu suka karanta wannan za su zarge ni da girman kai amma zancen ba haka ta ke ba.

"Dole ne mu sauke nauyin da ya rataya a kan mu, Sardauna da Murtala sun rasa rayyukan su domin shugabancin da Allah ya basu, saboda haka wannan nauyi ne akan mu na jagorancin al'umma domin mun fi kowa dacewa da ita a yanzu. Idan wadanda suka fi mu ilimi suka bayyana, nauyin zai koma kansu."

Labda ya cigaba da cewa makiyayan na bayar da himma wajen ilimin boko domin a baya iyayen su sun kyamaci bokon dalilin turawa kirista ne suka kawo shi. Ya kuma shawarci jihohin da ke kyamar bawa makiyaya filayen kiwo su canja shawara domin al'ummar su ne ke amfana da naman shanun ba makiyayan ba.

A gefe guda kuma tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya shawarci gwamnatin jihar Binuwai da Gwamnatin Tarayya su zauna a teburin sulha domin warware matsalar a maimakon nuna yatsa ga juna da sukeyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164