Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani Attajirin dan Kasuwa a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani Attajirin dan Kasuwa a Kaduna

- Masu garkuwa da mutane sun kutsa kasuwar tuna da Sheikh Abubakar Gumi inda suka sace wani dan kasuwa mai suna Alhaji Mukhtar

- Sun shigo kasuwar ne cikin mota suna ta harba harsashin bindiga a sama kuma suka nufi shagon nasa sukayi awon gaba dashi

- Daga bisani yan kasuwan sunyi kira ga Gwamnatin jihar ta Kaduna da Hukumomin Tsaro su taimaka wajen basu kariya daga afkuwar irin wannan fitina

A ranar Juma'a ne masu garkuwa da mutane suka sace wani fittacen dan kasuwa da ke sayar da sinadaren chemical mai suna Alhaji Muntari daga shogon sa da ke kusa da bakin dogo a kasuwar Sheikh Abubakar Mahmood Gumi da ke Kaduna.

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani Attajirin dan Kasuwa a Kaduna
Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani Attajirin dan Kasuwa a Kaduna

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Masu garkuwa da mutanen sun kutso cikin kasuwar ne da safiyar jiya a mota kirar Sharon, a yayin da suke shigowa suna ta harba bindiga sama har suka tafi dashi.

KU KARANTA: JNI tare da UNICEF za su yi hadin gwiwa don kawo karshen cin zarafin yara a Arewa

"Da shigowar su kasuwar, shagon sa suka nufa. Duk yadda akayi akwai wanda ke basu bayannan sirri kan sa domin akwai yan kasuwa da yawa a kasuwar amma shi kadai suka sace. Babu shaka akwai yadda suka san cewa kasuwancin sa na bunkasa," inji wani dan kasuwa.

Lamarin dai ya firgita yan kasuwa da wadanda suka zo siyaya hakan yasa kowa ya yi ta kansa a yayin da abin ke faruwa.

Hakan yasa yan kasuwan sukayi kira ga Gwamnatin Jihar da Hukumomin Tsaro su taimaka wajen ganin cewa sun kiyaye lafiya da dukiyoyin yan kasuwar da masu zuwa siyaya.

Har izuwa lokacin rubuta wannan rahoton, duk kokarin da akayi don ji ta bakin mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mukhtar Aliyu ya ci tura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164