Gwamna Masari zai kashe Biliyan 15.6 a kan titunan Katsina
- Mai Girma Masari zai kashe kudi wajen aikin titi a Katsina
- Gwamnatin Jihar za kuma ta gina wasu gidaje a fadin Jihar
- Kwamishinan ayyuka na Jihar Katsina ya bayyana wannan
Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari zai kashe makudan kudi wajen yin hanyoyi a fadin Jihar Katsina a wannan shekarar kamar yadda mu ka samu labari a karshen makon nan.
Katsina Post ta rahoto cewa Majalisar zartarwa ta Jihar Katsina tayi na'am da kashe sama da Naira Biliyan 15.6 wajen gina wasu sababbin hanyoyi a fadin Jihar inji Kwamishina aikace-aikacen Jihar Injiniya Tasiu Dandagoro.
KU KARANTA: Nan gaba za ma fara fitar da shinkafa har kasar waje
Kwamishinan Jihar ya bayyanawa manema labarai cewa titunan sun hada da na Tudun Iya Uwa Maska har Garin Dandume. Sannan kuma akwai hanyar da ta ratsa Kafur zuwa Malumfashi har zuwa Garin Dankanjiba da Mahuta.
Sauran hanyoyin sun hada da ta Garin Bakori zuwa Kadarawa da kuma ta Eka zuwa Yargamji da kuma wani titi ta Garin Mazoji. Gwamnatin Jihar za kuma ta gina gidaje har 150 a kan kudi kusan Naira Biliyan 2 a wannan shekarar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng