Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu

Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu

- Hukumar NACA ta ce adadin jarirai dake kamuwa da cutar kanjamau ya karu a jihar Gombe

- Hukumar NACA ta ce janye tallafi da suke samu daga babban bakin duniya ya sa yaduwar cutar ya karu

Hukuma yaki da cutar kanjamau a Najeriya (NACA) adadin jaririan da ake Haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu.

Wani jami’in hukumar NACA na jihar Gombe, Suraj Abdulkarim, yace babu abun da zai su iya tabukawa wajen hana yaduwar cutar a jihar Gombe saboda rashin kudi

Ya ce sun shiga wannan matsala ne sakamakon janye tallafin da suke samu daga kungiyoyin bada tallafi da babban bakin duniya.

Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu
Yawan jariran da ake haifa da cutar kanjamau a jihar Gombe ya karu

“Kudaden da muke samu daga kungiyoyin da babban bakin duniya ta kai miliyan 100 sannan tun da suke janye kudaden da muke da shi baya isar mu aiwatar da aiyukkan mu.

KU KARANTA : Wasikar Obasanjo zai taimakawa Buhari wajen samun nasara a zaben 2019

Abdulkarin ya ce duk da haka sun sami ragowar yaduwar cutar daga kashi 3.4% zuwa kashi 3.2% a shekara 2017.

Daga karshe ya yi albishir cewa da zaran sun sami kudaden da suke bukata za su inganta ayukkansu ne a yankunan karkara ta hanyar yiwa mata masu juna biyu gwajin cutar kanjamau domin kare jaririn dake cikin su

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel