Wata dattijuwa 'yar shekara 90 ta fara makarantar firamare
Ba bu shakka furfura ko yawan gemu ba sa hana mutum ya nemi ilimi, domin kuwa wata dattijuwa 'yar shekara 90, Priscilla Sitienei, wadda ta fito daga yankin Eldoret ta fara karatun ta a mataki na farko, inda ta shiga wata makarantar firamare a ƙauyen Uasin Gishu na ƙasar Kenya.
A cewar wannan dattijuwa, ta ga buƙaci fara makaranta domin ta samu ilimi da zai wadatar da ita wajen karanta littafin addinin ta da kuma karantawa tare da aika saƙonnin tas a wayar ta ta salula.
Priscilla ta shiga makarantar Vision Preparatory wadda take goga kafada da jikokinta guda bakwai a makarantar, inda ake mata laƙabi da sunan Goggo.
Legit.ng ta fahimci cewa, tun a lokacin da take shekara 65 da haihuwa, wannan dattijuwa ta shafe tsawon rayuwar ta ne wajen kula da ƙananan yara tun a yayin da take matar aure.
KARANTA KUMA: Makiyaya sun kai wani sabon hari jihar Binuwai
Goggo dai ba ta samu damar neman ilimi na zamani wadda ta faro rayuwarta ne tun a lokacin mulkin mallaka na turawa, inda a yanzu ta ga buƙatar hakan ba tare da jin kunya ko kulawa da abinda mutane zasu furta akan ta ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, malamin wannan makaranta ta Goggo take neman ilimi, sun yaba da irin hazakar ta da kuma irin yadda take jajircewa wajen neman ilimi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng