Yanzu Yanzu: Mutane 4 sun mutu, 10 sunji rauni, sannan an sanya ma gidaje wuta yayinda makiyaya suka kai hari jihar Plateau
Akalla mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan hari da makiyaya suka kai kauyen Josho, masarautar Daffo, karamar hukumar Bokkos dake jihar Plateau a daren ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
Majiyarmu ta Telegraph ta tattaro cewa mutane sama da goma sun jikkata yayinda aka sanya ma gidaje da dama wuta.
Da yake tabbatar da harin, hakimin kauyen na Daffo, Cif, Saf Dauda Maren ya ce harin ya biyo bayan wani sabani da ya shiga tsakanin makiyaya da mazauna garin akan wajen kiwo.
Kakakin yan sandan jihar Plateau, Mathias Terna wanda ya ce mutane uku ne suka mutu ya sanar da cewa an kama mutun daya dake da alaka da harin.
KU KARANTA KUMA: Ana siyar da wasikar da Obasanjo ya aika ga shugaba Buhari a Abuja
Bincike ya nuna cewa al’amura sun koma yadda su ke bayan zama da akayi tsakanin makiyaya da shugabanin garin Ron.
Za a ci gaba da zaman a yau domin guje ma ballewar sabon rikici.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng