Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na ganawa tare da Bola Tinubu da Bisi Akande
- Shugaba Buhari na ganawa tare da Bola Tinubu da Bisi Akande
- Ganawar na zuwa ne yan sa’oi kadan bayan Obasanjo ya bukaci Buhari da karda ya yi tazarce a 2019
Shugabna kasa Muhammadu Buhari na ganawa da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a fadar Aso Rock dake Abuja, a yau Talata, 23 ga watan Janairu.
A cewar Bashir Ahmad, Cif Bisi Akande wanda ya kasance jigon APC na cikin ganawar.
Shugabannin uku na ganawa mai muhimmanci ne a cikin sirri.
Koda dai ba’a bayyana dalilin ganawar ba tukuna, ganawar na zuwa ne yan sa’o’I kadan bayan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya saki wata wasika ga Buhari inda ya bukaci da kada ya sake takara a 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng