Daga zuwa zance ya fadi ya mutu a jihar Katsina
- Ana zargin saurayin da yi wa masoyiyar ciki
- 'Yan sanda sun tsare uban yariya da yarinyar
- Ance yana da farfyadiya, amma 'yan-sanda na tantama
A yankin Karaduwa, a jihar Katsina, watau a garin Funtuwa, hukuma ta tsare wata budurwa da mahaifinta, bayan da ake zargin iyayen yarinyar da kashe saurayinta wanda ake tantama ko yayi mata ciki ne.
Saurayin ya rasa ransa bayan da aka kaishi gida da rauni, daga gidansu masoyiyarsa, inda aka ce wai ya yanke jiki ya fadi ne, kuma dama yana da farfyadiya.
Sai dai kuma, masu bincike sun ce da walakin, inda ssuke duba ko marigayin ya sha duka ne wanda yayi sanadiyar mutuwarsa.
DUBA WANNAN: Sanata ya kai karar budurwarsa ta biya shi kudinsa
A yanzu dai za'a bincika gawar yaron dan jihar Zamfara, dan shekaru 22, sannan kuma za'a bincika ko yarinyar na dauke da juna biyu.
Su dai iyayen yarinya sunce ya fadi ne ya yanke da kyaure, bayan da aka gaya wa saurayin cewa bazai auri yarinyar ba, inda kuma wai shi ma yace ai ya riga yayi mata ciki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng